in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta fara amfani da sabbin fasahohin zamani wajen yaki da Boko Haram
2018-12-24 09:31:48 cri
Babban hafsan sojojin Najeriya Tukur Buratai ya ce Najeriya ta fara amfani da jirage marasa matuka da kuma sabbin fasahohin zamani wadanda ke da matukar tasiri wajen murkushe abokan gaba, a kokarin da ake wajen tarwatsa mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwar da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Lahadi, Buratai ya ce, a 'yan kwanakin nan sojojin kasar sun yi amfani da jirage marasa matuka wajen yin shawagi da gudanar da bincike, kuma wannan tsarin yana da matukar inganci a kokarin da ake wajen murkushe mayakan Boko Haram.

Haka zalika, ya ce, ko da kayan unifom na sojoji a yanzu haka suna amfani da fasahohin zamani inda aka sanya na'urar dake iya sanar da sojojin wasu bayanai da zarar an gano wata barazana.

"Fasahohin suna taka muhimmiyar rawa a yakin da ake, kuma ba za'a bar mu a baya ba," in ji hafsan sojojin.

"Muna da wani sashe mai kula da sauye-sauye da kirkire-kirkire wanda ke yin aikin nazari da bincike, ba ma kawai game da muhimman kayayyakin aiki ba, har ma da yadda za'a yi amfani da kayayyakin fasahar zamani wanda hakan zai ba mu damar gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata," in ji Buratai. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China