in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sudan ta kudu sun nemi afuwa bayan yakin basasar kasar
2018-12-08 17:15:02 cri
Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir da mataimakinsa Wani Igga sun kafa wani shirin gangamin neman hada kan jama'ar kasar da neman sulhuntawa tsakanin al'ummar kasar Sudan ta kudun tun bayan rarrabuwar kawunan da aka samu a kasar a sanadiyyar yakin basasar da ya addabi kasar cikin shekaru 5.

A cikin wasu sakonnin murya da aka nada wanda ake watsawa kai tsaye ta gidajen radiyoyin kasar, shugabannin kasar sun nemi al'ummar kasar Sudan ta kudun dasu rungumi dabi'ar tafiya a matsayin hanyar da zata daidaita tashin hankalin kasar.

Gangamin, wanda kungiyoyin addinan kasar ke jagoranta, ana yin amfani da manyan allunan talla da muryoyin da aka nada inda ake isar da sakonnin neman zaman lafiya a duk fadin kasar.

Sudan ta kudu ta tsunduma cikin yakin basasa ne tun a karshen shekarar 2013, tashin hankalin wanda ya haifar da karuwar 'yan gudun hijira mafi sauri a duniya.

MDD ta kiyasta kimanin mutane miliyan 4 ne daga Sudan ta kudu rikicin ya daidaita, kana ya raba su da matsugunansu inda suke neman mafaka a ciki da wajen kasar. Yarjejeniyar zaman lafiyar kasar wanda aka rattaba hannu kanta a watan Augastan 2015 ta wargaje a sakamakon barkewar sabon rikici a Juba a watan Yulin shekarar 2016.

Da alama sabuwar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rattaba hannu kanta a watan Satumban wannan shekara ana samun nasarori bayan da aka samun raguwar yawaitar kashe kashen rayukan jama'a a 'yan watannin da suka gabata a kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China