in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu rajin kare hakkin dan adam a Sudan ta kudu za su kawo karshen cin zarafin mata
2018-12-11 11:11:56 cri
Masu fafutuka a Sudan ta kudu sun sha alwashin daukar matakan shirya gangamin nuna adawa da banbancin jinsi da kuma cin zarafin mata a sanadiyyar wasu al'adun gargajiya da ake fakewa da su.

Masu fafutukar sun hada da masana daga bangaren makarantun ilmi da kungiyoyin fararen hula inda suka lashi takobin shirya gangamin nuna adawa da tsarin al'adun da nufin kawo karshen nuna bambancin jinsi da cin zarafin mata da 'yan mata a duk fadin kasar wanda ya samo asalin tun bayan barkewar yakin basasar kasar cikin shekaru 5 da suka gabata.

Ayak Chol Deng Alaak, wata mai rajin kare hakkin mata ta bayyana cewa, sabon gangamin da suka shirya zai kawo karshen mumunan al'adun kasar kamar auren wuri wanda ke tauye mata wajen hana su samun damammaki a fannonin rayuwa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China