A ranar 27 ga watan Disamban bara ne, hukumar zaben kasar Madagascar ta sanar da sakamakon kuri'un zaben shugaban kasar zagaye na biyu, inda Andry Rajoelina ya samu kashi 55.66 cikin dari, ya doke Marc Ravalomanana, abin da ya ba shi damar lashe zaben.
Bayan da hukumar zaben kasar Madagascar ta sanar da sakamakon zaben ne, magoya bayan Ravalomanana suka yi zanga-zanga cewa, an tabka magudi yayin da jefawa da ma kidaya kuri'un a zagaye na biyu, tare da kin amincewa da sakamakon zaben. (Zainab)