in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu kwararrun jami'an kasar Sin 4 sun isa Madagascar domin yaki da barkewar annoba
2017-10-29 12:53:02 cri
Tawagar kwararrun jami'an kasar Sin 4 sun isa birnin Antananarivo na kasar Madagascar domin tallafawa kasar, don yakar wata annobar cuta da ta barke a kasar.

Wang Jian, shi ne shugaban tawagar kwararrun likitocin na kasar Sin ya ce, sun ziyarci kasar ne domin tallafawa hukumar lafiya ta Madagascar ta kasar domin yakar annobar cutar da ta barke a kasar, ya kara da cewa, jami'an tagawar na kasar Sin za su bada horo na musamman a fannin kiwon lafiya ga jami'an kula da lafiya na Madagascar.

Ana sa ran tagawar jami'an za su yi musayar ra'ayoyi da jami'an kiwon lafiya na Madagascar da kuma sauran hukumonin kula da tsabta da na hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO), dake kasar.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Madagascar ta tabbatar da mutuwar mutane kimanin 126, kana wasu mutanen 1,292 kuma sun harbu da cutar annobar, wanda aka yi amanna ta barke a kasar tun a ranar 1 ga watan Agastan wannann shekara.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, kashi 65 cikin 100 na cutar annobar zazzabin ciwon sanyi ne, amma ba irin wacce aka saba gani ba.

Ita dai wannan annobar cutar, tana saurin kashe mutane, kuma cuta ce wacce ake yada ta daga wani mutum zuwa wani. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China