in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Madagascar ya bayyana zanga-zanagar bangaren adawa a matsayin yunkurin juyin mulki
2018-04-23 10:55:20 cri
Shugaban kasar Madagascar Hery Rajaonarimampianina ya bayyana zanga-zangar da bangaren adawa a kasar ya jagoranta ranar Asabar da ta gabata a birnin Antananarivo, a matsayin yunkurin juyin mulki.

Gwamnatin kasar ta ce akalla mutum guda ya ransa ransa, wasu 17 kuma sun raunata, yayin arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro, sai dai shugabannin 'yan adawan sun ce adadin wadanda suka mutu ya kai 6.

Masu zanga-zangar na adawa ne da sabuwar dokar zaben kasar, wadda suka ce za ta ware da yawa daga cikin 'yan takararsu tare da bada fifiko mai yawa ga jam'iyya mai mulki yayin zaben kasar dake tafe.

Shugaban ya ce jami'an tsaro za su kare tsarin demokradiyyar Madagascar da kuma al'umma da dukiyoyinsu.

Ya kara da cewa, kofarsa a bude take da a tattauna domin makomar kasar.

Tun bayan samun 'yancin kai a 1960, Madagascar ta fuskanci rikice-rikicen siyasa har sau 4 a shekarun 1972 da 1991 da 2002 da kuma 2009. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China