in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta baiwa Madagascar kayayyakin yaki da annoba da beraye ke yadawa
2017-11-09 10:22:54 cri
Jiya Laraba ne a birnin Antananarivo, hedkwatar kasar Madagascar, aka shirya bikin mika kayayyakin jin kai na gaggawa da kasar Sin ta bai wa Madagascar domin yaki da annobar cutar da beraye ke yadawa a da.

Firaministan kasar Solonandrasana Mahafaly Olivier, ministan harkokin kiwon lafiyar al'ummar kasar Lalatiana Andriamanarivo da sauran jami'an gwamnatin kasar, jakadar kasar Sin dake Madagascar, madam Yang Xiaorong, kungiyar masanan kasar Sin a fannin yin rigakafi da yaki da annobar da beraye ke yadawa tare kuma da kungiyar likitocin kasar Sin ne suka halarci bikin.

A jawabin da ya gabatar yayin bikin, a madadin gwamnatinsa, firaminista Solonandrasana Mahafaly Olivier ya gode wa gwamnatin Sin da kayayyakin da ta baiwa kasarsa a dai-dai wannan lokaci da take matukar bukata, tare da turo masana a fannin yin rigakafi da yaki da annoba wadda beraye ke yadawa.

Ita ma a nata jawabin madam Yang Xiaorong ta bayyana cewa, gwamnatin Sin ta sake bai wa Madagascar kayayyakin da darajarsu ta kai kudin Sin yuan miliyan 3, tare da turo masana da abin ya shafa 6, lamarin da ya shaida zumuncin da gwamnatin Sin da jama'arta suke nuna wa jama'ar Madagascar, kasar Sin na son hada kai da kasashen duniya, a kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan 'yan Adam. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China