in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ntsay ya kama aiki a matsayin sabon firaministan Madagascar
2018-06-07 09:29:03 cri
Sabon firaministan kasar Madagascar Christian Ntsay ya kama aiki, bayan shan rantsuwa gaban kusoshin gwamnati, da shugabannin rundunar sojin kasar, da kuma jami'an diflomasiyya. Christian Ntsay mai shekaru 57 da haihuwa, ya maye gurbin Olivier Mahafaly Solonandrasana.

Da yake gabatar da jawabi yayin bikin kama aiki a fadar gwamnatin kasar da ya gudana a jiya Laraba, Mr. Ntsay ya ce cikin manyana kudurori da zai sa a gaba akwai tabbatar da gudanar da ayyukan hukuma bisa tsari, da karbar gudummawa daga 'yan kasa tare, da gudanar da komai a bude. Kaza lika zai tabbatar da ana gudanar da zabubbuka kasar bisa gaskiya da adalci.

Ya ce bayan bayyana sunayen mambobin sabuwar gwamnati da za a yi nan ba dadewa ba, abu na gaba shi ne sanar da ranar gudanar da zabe. Har ila yau za a baiwa batutuwan tsaro, da yaki da cin hanci, da inganta harkokin kasuwanci, tare da raya yankunan kudancin kasar fifiko.

Sabon firaministan ya ce ya samu amincewar dukkanin sassan kasar, don haka zai bude kofar sa ga daukacin jam'iyyun siyasar kasar. Daga nan sai ya yi kira daukacin kawayen kasar ta Madagascar, da su tallafa mata da kudade da kwarewar aiki, ta yadda za ta kai ga cimma kudurorin da ta sanya gaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China