Shugabannin sun yi kiran ne yayin bikin cika shekaru 71 na barkewar rikicin nuna adawa da mamayar Faransa a kasar.
An gudanar da bukukuwa da dama a fadin kasar don tunawa da dubban mutanen da yakin ya rutsa da su.
A birnin Moramanga dake da nisan kilomita 110 daga babban birnin kasar Antananarivo, shugaban kasar Hery Rajaonarimampianina ya gudanar da bikin ajiye furanni a inda aka binne daruruwan 'yan kasar a makabartar wadanda suka sadaukar da kansu.
A cewar Shugaban, fadan da mazan jiyan suka yi ya nuna cewa hadin kai na da muhimmanci wajen ceton kasar.
A ranar 29 ga watan Maris din 1947 ne fadan nuna kin jinin Faransa ta barke a fadin Madagascar, inda rikicin ya fi kamari a birnin Moramanga. (Fa'iza Mustapha)