Firaministar Birtaniya Madam Teresa May, ta ce kasar ta za ta nace ga aiwatar da shirin hadin kai a dukkan fannoni na yarjejeniyar nukiliyar Iran, kuma ta jaddada yarjejeniyar a matsayin hanya mafi dacewa ta bunkasuwar makaman nukiliya a Iran. Madam Teresa May ta bayyana hakan ne yayin da take ganawa da firaministan Isra'ila Netayahu a wannan rana.
Kakakin fadar firaministan Birtaniya ya nuna cewa, yayin zantawar jami'an, Madam May ta bayyanawa Netayahu cewa, ta yi matukar damuwa game da hare-haren da ake kaiwa zirin Gaza a kwanakin nan.
An ba da labarin cewa, Netanyahu ya fara ziyararsa a Turai daga ran 4 ga wata, don yin iyakacin kokarin shawartar Jamus, Faransa da Birtaniya da su canja matsayin da suka dauka, wato yin watsi da amincewa da yarjejeniyar nukiliyar Iran. (Amina Xu)