in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatariyar cikin gida na Birtaniya ta yi murabus
2018-04-30 16:29:05 cri
Sakatariyar cikin gida ta Birtaniya Amber Rudd ta yi murabus daga aiki a daren jiya Lahadi, bayan matsin lamba da ta biyo bayan turkaturkar matsalar shige da fice da ta dabaibaye ofishinta. Tuni dai Firaminista Theresa May ta amince da takardar murabus din uwargida Rudd.

An dai ta kalubalantar ofishin Rudd, game da wata sanarwa da ofishin ta ya fitar a makwannin baya, wadda ke kunshe da wani shiri na fitar da wasu 'yan yankin kerebiya da suka shiga Birtaniya tun cikin shekarun 1960 daga kasar, duk kuwa da cewa an ba su izinin zama a kasar tun cikin shekarun 1970.

An dai ta kalubalantar wannan mataki wanda tuni Birtaniya ta ce kuskure ne kuma ta janye shi, tare da ba da hakuri game da waccan sanarwa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China