in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Faransa ya bayyana garkuwa da mutane gami da harbe-harben da aka yi a kasar a matsayin harin ta'addanci
2018-03-24 13:55:32 cri
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da cewa, harbe-harbe gami da garkuwar da aka yi da wasu mutane a wani kanti jiya a garin Trebes dake kudancin kasar, hari ne irin na masu tsattsauran ra'ayin addini.

Emmanuel Macron ya ce, kasarsa ta fuskanci harin ta'addanci, inda ya ce an gano dan ta'addan har ma an kashe shi yayin samamen da aka kai.

Shugaban na Faransa ya kara da cewa, an kashe mutane uku tare da jikkata wasu 16, ciki har da wani babban jami'in dan sanda. Kuma daga cikin wadanda suka jikkata, mutane biyu na cikin halin rai kwaikwai mutu kwaikwai.

Da safiyar jiya Jumma'a ne, Redouane Lakdim, mai shekaru 26 da haihuwa, ya kashe wani mutum guda, gami da raunata wani daban kafin ya sace wata mota. Daga bisani kuma, ya bude wuta kan wasu jami'an 'yan sanda da suke motsa jiki a Carcassone, lamarin da ya kai ga jikkata guda daga cikinsu. Daga can kuma ya je garin Trebes, inda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu kafin daga bisani a harbe shi har lahira.

Kungiyar IS dai ta yi ikirarin kai harin. Inda shugaba Macron ya ce, hukumomin tsaron Faransa na gudanar da bincike kan sahihancin ikirarin.

Kasar Faransa ta sha fama da hare-haren ta'addanci, musamman ma bayan da ta dauki matakan soji a kasashen Siriya da Iraki da kuma yankin Sahel.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China