Yayin taron, Macron ya gabatar da wani jawabi, yana mai cewa, ya kamata kasashen duniya daban-daban su samu bunkasuwa, wato kar wata kasa daya kadai ta nuna fin karfin ta, al'amarin da ya nuna cewa, Faransa na son fitar da tarayyar Turai daga mawuyacin halin da take ciki a yanzu.
Macron ya ce, gwamnatin Amurka na kokarin nuna fin karfinta a duk fadin duniya, duk da cewa shugabannin kasashen Faransa da Jamus da na tarayyar Turai, sun ziyarci Amurka sau da dama don tattaunawa da shugaba Donald Trump, amma hakan bai yi amfani sam.
A cikin jawabin na Macron, yayin taron jakadun kasar Faransa dake kasashen waje, ya yi suka game da abun da Trump ke yi na nuna fin karfin kasarsa, kana ya yabi kwazon kasar Sin, bisa shigar ta cikin harkokin duniya dake kunshe da bangarori daban-daban. Macron ya ce zai yi kokarin yin shawarwari tare da kasar Sin, don kare muradun kasarsa.(Murtala Zhang)