in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Libya sun yi gargadi game da shirya kuri'ar raba gardama game da kundin tsarin mulkin kasar
2018-12-07 20:08:41 cri
A jiya ne, hukumar zartaswar koli ta kasar Libya ta yi gargadi game da hanzarin shirya kuri'ar raba gardama kan kundin tsarin mulkin kasar, matakin da ta ce zai iya haifar ga kalubale ga kundin tsarin mulkin kasar.

Hukumar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, yanzu haka ana tattaunawa a kan daftarin kundin tsarin mulkin kasar. Sanarwar hukumar dai na zuwa ne bayan da shugaban hukumar zaben kasar Imad Al-Sayah ya sanar da cewa, za a shirya kuri'ar raba gardama game da kundin tsarin mulkin kasar na din-din-din kafin karshen watan Fabrairun shekarar 2019 dake tafe. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China