Harin wanda aka kai da yammacin ranar Asabar a kauyen Magami dake gundumar Faru a karamar hukumar Maradun na jahar Zamfara, harin ya zo ne kasa da mako guda bayan wani harin da aka kai wani yanki dake jahar wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutane 25.
Kakakin hukumar 'yan sandan jahar Zamfara Muhammed Shehu, ya ce an tura karin jami'an 'yan sanda zuwa yankin domin hana sake kaddamar da wani harin a yankin.
Jami'an gwamnati da dama, har da mukaddashin gwamnan jahar Zamfara, Sanusi Rikiji, sun halarci jana'izar wadanda harin ya rutsa da su a jiya Lahadi. (Ahmad Fagam)