in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta tsaurara matakan tsaro a filayen saukar jiragen sama gabannin bikin Kirismeti
2018-12-23 16:16:02 cri
Hukumomin Najeriya sun tsaurara matakan tsaro a dukkanin filayen saukar jiragen sama a fadin kasar gabannin bikin Kirismeti gami da bukukuwan sabuwar shekara ta 2019.

Bisa wata sanarwar da aka bayar ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua jiya Asabar, mai magana da yawun hukumar kula da filayen jiragen sama ta tarayyar Najeriya wato FAAN, Madam Henrietta Yakubu ta tabbatarwa fasinjoji da sauran mutanen da suka je filayen saukar jiragen sama samun cikakken tsaro a yayin bikin Kirismetin.

A cewarta, dukkanin filayen jiragen saman Najeriya a shirye suke wajen tinkarar cunkoson zirga-zirgar fasinjoji da ake iya samu a yayin bikin.

Madam Henrietta Yakubu ta kara da cewa, an riga an dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaro ga zirga-zirgar fasinjoji gami da hajjoji a daukacin filayen jiragen saman Najeriya a yayin bikin Kirismetin na bana.

Har wa yau, 'yan sandan kasar sun yi gargadi ga jama'a da kada su yi wasa da abubuwan wuta, inda a cewarsu, har yanzu ana ci gaba da aiwatar dokar haramta amfani da abubuwan fashewa.

Ita ma a nata bangaren, kakakin 'yan sandan Najeriya Irene Ugbo ta ce, ana nan ana ci gaba da amfani da dokar haramta sayar da abubuwan fashewa da na wuta a yayin bukukuwan Kirismetti da sabuwar shekarar. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China