in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayaka masu samun goyon bayan Al-Qaida sun fafata da dakarun da Turkiyya ke marawa baya a Syria
2019-01-02 11:09:02 cri
Fada ya runcabe a jiya Talata, tsakanin mayakan dake samun goyon bayan kungiyar Al-Qaida, da dakarun da kasar Turkiyya ke marawa baya a lardin Aleppo na kasar Syria.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi dauki ba dadi na tsawon lokaci, lokacin da mayakan kungiyar Hayat Tahrir al-Sham suka kaddamar da farmaki, kan wasu yankunan dake karkashin ikon dakarun "National Liberation Front" mai samun goyon bayan gwamnatin Turkiyya a wajen birnin Aleppo, inda dakarun na Hayat Tahrir al-Sham suka kwace iko da wasu garuruwa guda biyu.

A cewar kungiyar dake sa ido game da kare hakkokin bil Adama ta kasar, yara biyu sun rasa rayukansu yayin dauki ba dadin. Kaza lika mayakan wata kungiyar mai suna Ansar al-Din, sun yi yunkurin shiga tsakani cikin fadan, inda daga karshe suka dakatar da musayar wuta a yankin na yammacin Aleppo.

A wata Oktoba da ya gabata ma dai kungiyoyin dake adawa da juna a yammacin Aleppo, sun yi dauki ba dadi da juna, biyowa bayan kisan dakarun kungiyar Hayat Tahrir al-Sham da mayakan dake samun goyon bayan Turkiyya suka yi a arewacin kasar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China