Jami'in ya yi wannan kira ne yayin taron kwamitin sulhu na MDD da aka yi kan yanayin da Syria ke ciki.
Ya kara da cewa, akwai bukatar taimakawa kokarin gwamnati da al'umma na sake gina kasar, yana mai cewa ya kamata kasashen duniya su marawa gwamnatin kasar baya a kokarin da take na samar da kayayyakin jin kai ga fararen hula dake cikin mawuyacin hali tare da kara tsayuwar daka wajen yaki da barazanar ta'addanci a kasar. (Fa'iza Mustapha)