Da yake tsokaci ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua game da hakan, jami'i a ofishin jakadancin Sin dake birnin Damascus Ma Xuliang, ya ce wannan tallafi zai yi tasirin gaske, wajen farfado da yanayin zamantakewar al'ummar Syria, da kyautata ababen more rayuwar su, da kuma inganta fannin samar da hidima.
Jami'in ya kuma jaddada cewa, tallafin na baya bayan nan, na cikin jerin taimako da Sin ke gabatarwa, don ba da gudummawa wajen sake ginin kasar ta Syria. Ya ce a nan gaba, Sin za ta ci gaba da samar da tallafin jin kai ga kasar.
Shi kuwa a nasa bangaren, mataimakin ministan ma'aikatar lantarki ta kasar Syria Nidal Qarmoushi, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, taimakon kayayyakin samar da lantarki na Sin, ya zo ne a daidai gabar da ake matukar bukatar sake gina ababen more rayuwa a kasar. (Saminu Hassan)