Staffan de Mistura ya bayyana hakan ne ta kafar talabijin daga birnin Geneva, ga zauren kwamitin tsaron MDD a jiya Litinin, yana mai cewa fatansa shi ne kafin karshen watan Disamba mai kamawa, za a kai ga gudanar da zama na farko na wannan kwamiti.
Bisa ka'ida wa'adin aikin Staffan de Mistura zai kammala ne a karshen watan nan, amma ya ce zai ci gaba da zama kan mukamin sa, har ya zuwa wata mai zuwa domin yin hobbasa na karshe, domin cimma burin kafuwar wannan kwamiti. Jami'in ya kara da cewa, MDD ta shirya tsaf, domin ba da dukkanin gudummawa ta kafuwar kwamitin, ko da yake dai bai kore yuwar gamuwa da cikas a aikin da ake yi a yanzu ba.
A jawabin sa na karshen cikin wata mai zuwa ga zauren kwamitin tsaron MDD, de Mistura zai yi karin haske, game da inda aka tsaya a aikin kafuwar kwamitin tsara kundin mulkin kasar ta Syria.
Babban magatakardar Antonio Guterres ya riga ya bayyana sunan Geir Pedersen daga kasar Norway, a matsayin wanda zai maye gurbin de Mistura. (Saminu Hassan)