in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Ya kamata a yi amfani da damar sassaucin yanayin da Sham ke ciki wajen farfado da yunkurin shimfida siyasa
2018-10-18 13:42:14 cri

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Ma Zhaoxu ya ba da jawabi a yayin taron kwamitin sulhu kan yunkurin shimfida siyasa a kasar Sham wato Syria wanda aka gudanar a jiya Laraba, cewar shawarwari a siyasance hanya ce daya tilo da ke iya warware matsalar kasar Sham, ya kamata kasashen duniya su yi amfani da damar sassaucin yanayin da Sham ke ciki wajen sake farfadowar yunkurin shimfida siyasa a kasar.

Ma ya kuma kara da cewa, ko da an samu ci gaba wajen yunkurin a 'yan kwanakin baya, amma ana fuskantar kalubale. Abin da yake gaban komai shi ne a kafa kwamitin kundin tsarin mulkin Sham wanda zai kunshi bangarori daban daban, da ma samun amincewar sassa daban daban na kasar.

A karshe dai Ma ya ce, kasar Sin na son yin kokari tare da kasashen duniya wajen sa kaimi ga yunkurin shimfida siyasa a kasar Sham, ta yadda za a kyautata halin jin kai da kasar ke ciki, da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, da ma yanayin da kasar ke ciki tun da wuri.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China