in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar kawancen Amurka ta kaddamar da hari kan wani sansani na dakarun gwamnatin Syria
2018-12-03 09:47:36 cri
Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na kasar Syria SANA na cewa, rundunar kawancen dakarun soji da Amurka ke jagoranta, ta kaddamar da hari kan wani sansani na dakarun Syria dake garin Sukhneh a gabashin lardin Homs.

SANA ya tabbatar da aukuwar wannan hari na yammacin jiya Lahadi, sai dai kuma ya ce ba a samu asarar rayuka yayin harin ba. Harin dai na makamai masu linzami, an yi nufin ya sauka kan wani sansani na sojojin dake lardin na Homs, to sai dai babu wasu cikakkun bayanai daga tsagin gwamnatin kasar game da aukuwar sa.

A wani ci gaban kuma, wani tsagi na masu fafutuka dake kasar ya bayyana cewa, an kaddamar da harin ne kan wani ayari na sojojin gwamnatin Syria a kusa da hamadar Homs, bisa kusantar da suka yiwa sansanin Amurka dake yankin. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China