in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libiya: Masu zanga zanga sun yi bore a helkwatar gwamnati dake birnin Tripoli
2018-12-03 09:34:36 cri
A jiya Lahadi ne dandazon masu zanga zanga suka yiwa fadar gwamnatin Libya dake birnin Tripoli kawanya, a wani mataki na yunkurin tursasawa gwamnati ta amince da inshorar lafiya, da biyan albashin ma'aikata yadda ya kamata.

Rahotanni sun ce masu zanga zangar sun kunshi abokai ko 'yan uwan wadanda suka jikkata, da ma wadanda suka rasa rayukansu, yayin juyin juya halin kasar, inda suka rika bayyana bukatunsu na biyan albashi, da kudaden magani ga wadanda lamarin ya shafa.

An ce wani sashe na dandazon masu zanga zangar sun karya kofar helkwatar suka kuma shiga cikin ta. Daga bisani mataimakin firaministan kasar Ahmad M'etig, ya zanta da su, tare da sauraron bukatunsu.

Wata kafar watsa labarai dake birnin ta wallafa hotunan masu zanga zangar dauke da alluna masu kunshe da bukatun su, wasun su a cikin helkwatar gwamnatin, wasu kuma a farfajiyarta. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China