in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta dauki matakan shawo kan kalubalolin tsaro a kasar
2018-12-23 15:15:21 cri
Ministan tsaron Najeriya Mansur Dan-Ali ya ce, kasar ta dauki kwararan matakai domin shawo kan matsalar kalubalolin tsaro domin kare kasar daga duk wasu hare hare na ciki gidan da wajen kasar.

A wata sanarwa da aka aike kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Asabar, ministan ya ce, matsalar shaye-shayen kayan maye, rashin aikin yi, da rashin shugabanci na gari su ne ummul aba'isin dake haifar da tabarbarewar tsaro a yankin arewacin Najeriya, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki da su hada kansu domin daukar kwararan matakan don shawo kan matsalolin.

Ya ce daga cikin matakan da gwamnati ta dauka sun hada da kirkiro runduna ta 8 ta dakarun sojojin Najeriya a jahar Sokoto domin warware kalubalolin tsaro a shiyyar arewa maso yammacin kasar, musamman a jahohin Zamfara da Kaduna.

Ministan ya ce, samar da irin wannan runduna a Gusau, babban birnin jahar Zamfara da kuma wata a yankin birnin Kebbi, zai yi matukar taimakawa wajen shawo kan matsalolin tsaro a shiyyar.

Dan Ali ya ce, a kwanan nan an tura dakarun sojoji 500 da kuma wasu jami'an tsaro 500 zuwa yankin inda za su gudanar da wani aikin wanzar da tsaro na hadin gwiwa mai taken "SHARAN DAJI" da nufin kakkabe ayyukan 'yan bindiga da sauran kalubalolin tsaro dake addabar jahohin Zamfara da Kaduna da ma shiyyar baki daya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China