Adadin kasuwannin kasar Sin sun karu matuka daga kasuwanni dubu 490 a farkon aiwatar da shirin gyare gyaren da bude kofa, zuwa kasuwanni miliyan 109 ya zuwa karshen watan Nuwambar wannan shekara, Ma Zhengqi, mataimakin shugaban hukumar sa ido kan yadda ake yin kasuwanci na kasar Sin, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai.
Bisa ga alkaluman kididdigar da aka samu ya nuna cewa, adadin kasuwannin daidaikum mutane da kasuwanni masu zaman kansu ya kai kashi 95 bisa 100, sannan da kashi 60 bisa 100 na kudaden GDP na kasar kana sama da kashi 80 bisa 100 na yawan ayyukan yi da aka samar a biranen kasar, in ji Ma.
A yayin da kasar Sin ke kokarin neman sauya tsarin bunkasa tattalin arzikinta wanda zai kara janyo hankula daga bangarorin ayyukan ba da hidima, manyan masana'antu suna kara samun bunkasuwa cikin sauri, inda aka samu karuwar adadin kasuwannin wannan fanni da kashi 77 bisa 100.
Ma ya ce, gwamnatin Sin za ta ci gaba da daukar matakan kyautata yin gyare gyare domin daidaita dokoki, da tafiyar da sha'anin mulki, da inganta dokokin, da kyautata ayyukan ba da hidima, da kuma zurfafa yin gyare gyare da nufin inganta samar da muhallin kasuwanci a kasar. (Ahmad Fagam)