Kididdigar da ma'aikatar masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta fitar, na nuni da cewa, harkokin kasuwanci ta intanet a kasar, sun habaka hanyoyin samun kudin shiga cikin sauri a watanni hudun farko na bana.
Manyan harkokin kasuwanci da na kamfanoni masu samar da hanyoyin intanet, sun samu karin kudin shiga zuwa kaso 24.9 a kan na bara, inda adadin ya kai yuan biliyan 264.9, kwatankwacin dala biliyan 41.4, a tsakanin watannin Janairu da Afrilu.
Ma'aikatar ta ce, adadin a bana, ya karu da kaso 5.4 bisa dari a kan na makamancin lokacin na bara.
Bangaren wasanni ta intanet wato game, da na cinikayya, sun ci gaba da fadada cikin sauri, inda kudin shigar da bangaren game ya samu ya karu zuwa kaso 27.9 bisa dari a kan na shekarun baya, adadin da ya kai yuan biliyan 58.7. Kudin shigar cinikayya ta intanet ya tashi zuwa kaso 40.4 bisa dari, inda ya kai yuan biliyan 92.3.
A cikin watannin, masana'antar intanet ta zuba jarin yuan biliyan 14.5 cikin harkokin bincike da na ci gaba, wanda ya karu da kaso 22.3 bisa dari a kan na shekarun baya.
A cewar ma'aikatar, bangaren na intanet ya zama wani bangare na sabon tattalin arzikin kasar Sin, a daidai lokacin da fasaha da kayayyakin amfani ke jagorantar bunkasar tattalin arzikin kasar. (Fa'iza Mustapha)