Rahoton bankin kan yanayin ksuwanci na shekara-shekara, ya ce a bana, kasar Sin ita ce ta 46, inda ta tashi daga matsayi na 78 da ta kasance a bara, la'akari da dimbin sauye-sauyen da ta aiwatar a yankin gabashin Asiya da Fasifik.
Shugaban Bankin a kasar Sin Bert Hofman, ya ce Sin ta samun ci gaba sosai wajen inganta yanayin harkokin kanana da matsakaitan sana'o'i a bara. Ya ce ci gaban alama ce dake nuna darajar da Gwamnatin kasar ta ba batun bunkasa kasuwanci. (Fa'iza Mustapha)