A kwanan baya, ma'aikatar kasuwancin kasar Amurka ta sanyawa kamfanin Jinhua na lardin Fujian mai samar da kayayyakin wutar lantarki a cikin jerin sunayen da take son kakkabawa takunkumi. Don haka, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya nuna adawa da kasar Amurka ta yi amfani da ma'anar tsaron kasa da matakan kayyade fitar da wasu kayayyaki kamar yadda take so a fannoni maras ruwa da tsaki, ya kuma nemi bangaren Amurka da ya dakatar da matakin sanya takunkumi bisa dokarsa kawai, kuma ya dakatar da tsoma baki kan cinikayya da hadin gwiwar da kamfanoni daban daban suke yi yadda ya kamata. (Sanusi Chen)