Mai magana da yawun ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Gao Feng, ya ce Sin za ta dauki karin matakai na samar da daidaito da ingancin sayayya a cikin gida.
Gao Feng ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin wani taron 'yan jarida da ya gudana a nan birnin Beijing. Ya ce bunkasa harkar sayayya a gida muhimmin sashe ne na ayyukan hukuma. Ya ce a nan gaba za a aiwatar da matakai na samar da kyakkyawan yanayi na gudanar da hada hada a yankunan karkara da birane, da kara samar da kayayyaki da ake bukata a matsakaici da doguwar bukata, ta hanyar karo kayayyakin da ake shigo da su daga waje, tare da kara yawan irin wadannan hajoji da ake shigarwa birane gwargwadon bukata.
Kaza lika a cewar jami'in, kasar ta Sin za ta kara inganta hanyar samar da kayayyaki ta hanyar tabbatar da nagarta da muhalli mai kyau na hada hadar su.
Ya ce sayen hajoji daya ne daga muhimman hanyoyin bunkasa tattalin arziki. Inda a shekarar da ta gabata, matsayin hakan ya karawa ma'aunin GDP kasar ta Sin kaso 58.8 bisa dari.(Saminu)