Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake aiki a Libya UNSMIL, ya yi tir da kashe-kashen mutane dake karuwa cikin makonnin da suka gabata a Tripoli, babban birnin Libya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, shirin ya ce yana ci gaba da karbar rahotannin 'yan bindiga dake aiwatar da kisa a Tripoli, yana mai jadadda cewa ya kamata a rika shigar da kararraki da sabanin tsakanin mutane gaban kotu, maimakon daukar doka a hannu.
Shirin ya kuma yi kira ga hukumomi a kasar, su gaggauta daukar ingantattun matakan kare mutane daga irin wannan kisa, tare da aikewa da sako cikin babbar murya cewa, ba za a lamunci ayyukan ba, sannan a nuna da gaske ake, ta hanyar gudanar da cikakken bincike don ganowa da hukunta wadanda ke aikata laifin. (Fa'iza Mustapha)