A cikin sakon nasa, Li ya ce, tun lokacin da kasar Sin da Sao Tome da Principe suka kulla huldar diplomasiyya, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu take ci gaba da kara bunkasa tare da zurfafa mu'amalar siyasa da kuma fadada hadin gwiwar kasashen biyu daga dukkan fannoni, wanda hakan ya kawo babbar moriya ga al'ummomin kasashen biyu. (Ahmad Fagam)