Yayin ziyarar ta sa, Mr. Li ya halarci taro na 21, na shugabannin Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN, da kuma taro karo na 21 a tsakanin shugabannin kasashen kungiyar ASEAN da kasashen Sin da Japan, da Koriya ta Kudu. Har ila yau, ya halarci taro karo na 13 na shugabannin kasashen gabashin nahiyar Asiya.