Ya zuwa watan Oktobar shekara ta 2018, adadin yawan kamfanonin Sin da baki 'yan kasuwa suka zuba jari a ciki ya tasamma dubu 950, kuma jimillar jarin wajen da ake amfani da shi a kasar ya zarce dala triliyan 2.1, al'amarin da ya nuna cewa, jarin waje ya riga ya zama babban karfi ga ci gaban tattalin arziki gami da zaman rayuwar al'umma a kasar ta Sin. Tun da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, kawo yanzu, Sin ta kafa wani cikakken tsarin doka kan harkokin zuba jari na baki 'yan kasuwa, wanda ke kunshe da dokokin da suka shafi kamfanonin hadin-gwiwar jarin Sin da na waje, da kamfanonin jarin waje da sauransu. Duk wadannan dokoki na bayar da tabbaci sosai ga ayyukan fadada bude kofa ga ketare gami da amfani da jarin waje. (Murtala Zhang)