Hua ta bayyana haka ne a yayin da take amsa tambayoyi game da wani rahoto da cibiyar hada hadar cinikayya ta Amurka dake kasar Sin ta bayar a yau. A cikin rahoton an ce, yawancin masana'antun kasar Amurka na da kyakkyawan fata game da makomar tattalin arzikin kasar Sin, amma wasu sun bayyana cewa, sun gamu da rashin adalci a kasar. Game da haka, Hua ta ce, kasar Sin na da babbar kasuwa a cikin gida, hakan kuma ya samar da damar samun bunkasuwa ga masana'antun kasashe daban daban, ciki har da Amurka. Kuma duk masana'antu da masu masana'antu suna iya ganin irin makoma mai kyau. (Bilkisu)