Rahoton da hukumar ta wallafa wanda ya yi nazarin yanayin harkokin zuba jari, ya ce adadin jarin da ake zubawa a kasashen ketare ya sauka da kaso 41 cikin dari, zuwa dala biliyan 470, daga dala biliyan 794 da ya kasance a makamancin lokacin a shekarar 2017.
Rahoton ya alakanta koma bayan da aka samu da matakin da kamfanonin Amurka suka dauka na karbo ribarsu da ya taru daga rassansu dake kasashen ketare, biyo bayan sauyin tsarin haraji.
Daraktan sashen zuba jari da kasuwanci na hukumar James Zhan, ya ce ana samun karuwar zuba jari a kasar Sin duk da takkadamar cinikayya da karuwar farashin sarrafa kayayyaki.
Kasar Sin ce kan gaba wajen samun jarin kasashen ketare, inda adadin ya karu da kaso 6, Birtaniya ke rufa mata baya da dala biliyan 66, sai Amurka da ta samu jarin dala biliyan 46. (Fa'iza Mustapha)