A yayin taron da ma'aikatar kasuwanci ta kira a wannan rana dangane da harkokin jarin waje na shekarar 2017, Mr. Zhong Shan ya yi nuni da cewa, za a mai da hankali wajen bunkasa yankunan ciniki maras shinge na gwaji a shekarar 2017 tare da ci gaba da kyautata yanayin kasuwanci da sassan da ke shigo jarin waje da kuma hanyoyin shigo jarin waje, domin tabbatar da shigo karin jarin waje yadda ya kamata a shekarar 2017. (Lubabatu)