in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta dauki karin matakai na janyo jarin waje
2016-12-30 09:48:50 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce majalissar zartaswar kasar ta amince da daukar matakan bunkasa janyo jarin waje cikin kasar, ta hanyar samar da sabbin ka'idoji, wadanda za su karfafa gwiwar masu son zuba jari a kasar.

Mr. Li Keqiang ya bayyana hakan ne bayan taron majalissar da ya jagoranta, yana mai cewa, an amince da wannan mataki ne domin cimma nasarar bunkasa hada hadar kasuwanci, da zuba jari, tare da kara bude kofa ga kasashen waje.

Ya ce, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da bunkasa bisa dabarun kara bude kofa ga kasashen ketare. Kuma baya ga fannonin fasaha da na gudanarwa, Sin na fatan janyo karin kudade domin fadada jarin a wasu sauran fannoni.

Li ya kara da jaddada kudurin gwamnatin Sin mai ci, na tabbatar da ana bin ka'idojin hukuma, wajen shigo da jari, yayin da a hannu guda ake daukar karin matakai na rage kudaden da ake kashewa wajen aiwatar da hakan.

Sababbin ka'idojin da aka tanada domin hakan dai za su magance wahalhalu da masu zuba dari a cikin kasar ta Sin ke fuskanta a wasu fannoni, ciki hadda harkar sufurin jiragen kasa, da kirar babura, da sarrafa makamashin ethanol.

Kaza lika masu zuba jari na iya shiga harkokin da suka jibanci samar da makamashi, da kare albarkatun ruwa, da kula da muhalli, da ma fannin samar da hidima ta ababen bukatu na yau da kullum, karkashin ingantattun dokoki.

Har wa yau a karan farko, masu zuba jari daga ketare za su iya shiga harkokin kidayar alkaluman kudade da tantance su. Sai kuma fannin zane zanen gine gine, da shirye shiryen kasar a fannin kimiyya da fasaha, wanda masu zuba jarin za su iya sanya kudade kamar sauran takwarorin su na gida, bisa babbar manufar kasar ta cimma muradun samar da kaya masu nagarta da aka yiwa lakabi da "Made in China 2025 Strategy".(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China