Alkaluman baya-bayan nan da ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, bisa hasashen da aka yi, a tsawon shekara ta 2016, baya ga fannonin banki, hannayen jari da inshora, jimillar kudin jarin waje da kasar Sin ta jawo ya kai kimanin Yuan biliyan 785, lamarin da ya sa kasar Sin shigewa gaba a dukkan kasashen dake tasowa a fannin cikin jerin shekaru 25.
Kasar Sin tana kara kyautata tsarinta na jawo jarin waje a sana'o'i da dama, wato daga sana'ar kere-kere ta gargajiya zuwa sana'ar kere-kere ta zamani.
A wani labarin kuma, sabon sakamakon bincike da taron kula da cinikayya da ci gaba na majalisar dinkin duniya ya fitar, ya yi nuni da cewa, a bana da badi, kasar Sin na ci gaba da zama kasa ta farko, wadda ke da makoma mafi kyau wajen jawo jarin waje a duk duniya.(Murtala Zhang)