in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an MDD sun damu kan rahoton cin zarafin mata a Sudan ta kudu
2018-12-06 09:42:59 cri
Manyan jami'an MDD da na kungiyar tarayyar Afrika (AU) sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da wani rahoton da ya shafi yadda aka ketawa mata haddi ta hanyar yin lalata da matan da 'yan mata sama da 150 a Sudan ta kudu, inda ya bukaci gwamnati da ta dauki matakan da suka dace, kakakin MDD ne ya sanar da hakan a jiya Laraba.

Stephane Dujarric ya ce, tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD a Sudan ta kudu (UNMISS) ta bada rahoto game da yadda aka ci zarafin mata da 'yan mata a lokacin da suke kan hanyarsu daga kauyukansu zuwa garin Bentiu dake shiyyar Unity, yankin dake karkashin ikon gwamnati a shiyyar arewacin kasar, a wasu kwanaki da suka gabata.

Dujarric ya ce, babban sakataren MDD mai kula da shirin wanzar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix, da Ambassador Smail Chergui, kwamishina na AU mai kula da zaman lafiya ta tsaro, da kuma babbar daraktar al'amurran mata a MDD Phumzile Mlambo-Ngcukaz, sun bayyana takaicinsu dangane da yadda aka ci zarafin mata ta hanyar lalata da fyade, wanda aka kiyasta yawan mata da 'yan mata da aka ci zarafinsu sama da 150 a baya bayan nan a kusa da garin Bentiu," a cewar Dujarric.

Wadanda suka afkawa matan wasu matasa ne maza sanye da kayan fararen hula ko kuma rigar soja," in ji UNMISS. "shirin wanzar da zaman lafiyar MDDr ya tura jami'an sintiri zuwa yankin da kuma jami'an kare hakkin bil adama domin su gudanar da bincike domin zakulo wadanda keda hannu wajen aikata cin zarafin." (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China