in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin jiragen saman Najeriya ya sanya hannu kan yarjejeniyar sayen jiragen Boeing 737 100
2018-12-22 16:25:55 cri

A karon farko kamfanin jiragen sama na Najeriya mai suna Green Africa Airways ya sha alwashi sayen manyan jiragen sama guda 100 samfurin 737 Boeing MAX 8 aircraft a wani babban yunkuri da ya yi, wanda zai kashe kimanin dala biliyan 11.7. Wani babban jami'in kamfanin samar da jiragen saman Amurka na Boeing shi ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a.

An kasafta tsarin ciniki ne zuwa jirage 50, a yayin da kamfanin jiragen na Najeriyar yake shirye shiryen fara ayyukansa da zummar kafa wani babban kamfanin sufurin jiragen sama mafi girma wanda zai karade nahiyar Afrika baki daya, ciki har da kasuwannin cikin gidan Najeriyar, inji kamfanin na Boeing.

Shirin wanda aka tsara shi tun a shekarar 2016, yana da helkwatarsa a Lagos, birnin kasuwancin Najeriya kuma birni mafi girma a nahiyar Afrika, kamfanin na Green Africa Airways tuni ya riga ya samu lasisin fara aikin daga mahukuntan Najeriya.

Shugabannin rukunin kamfanin sun hada manyan jami'an kamfanin karkashin jagorancin Tom Horton, tsohon shugaban kamfanin American Airlines, da William Shaw, tsohon shugaban kamfanin VivaColombia, da kuma Virasb Vahidi, tsohon jami'i a kamfanin jiragen sama na American Airlines. (Ahamd Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China