in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan Najeriya sun damke kwamandan Boko Haram
2018-12-22 20:32:48 cri
Wani babban kwamandan mayakan Boko Haram wanda ake nema ruwa a jallo, mai suna Umar Abdulmalik, tare da wasu mutane 7 da ake zarginsu da hannu wajen shirya mummunan harin bam na Abuja a shekarar 2015 sun shiga hannun jami'an 'yan sandan Najeriyar, inji kakakin hukumar 'yan sandan.

Abdulmalik wanda rundunar 'yan sanda ta musamman mai tattara bayanan sirri (IRT) ta cafke, a ranar Alhamis data gabata a yankin Ibafor dake jahar Legas, a yayin da yake karbar magunguna na raunukan da ya samu na harsasai a lokacin da aka yi arangama tsakanin mayakan 'yan ta'adda da jami'an 'yan sandan a ranar 26 ga watan Nuwamba a Abuja. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China