in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan bindiga sun halaka mutane a kalla 25 a arewacin Najeriya
2018-12-21 19:30:54 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla mutane 25 sun rasa rayukansu kana wasu da dama kuma sun jikkata, sakamakon wani hari da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kai a karamar hukumar birnin Magaji dake jihar Zamfara a yankin arewacin kasar.

Harin na ranar Laraba da maharan suka kai a yankin, shi ne na baya-bayan a jerin hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa yankin arewa maso yammacin kasar cikin watanni 6 da suka gabata.

Mazauna yankin sun bayyana cewa, galibin wadanda harin ya rutsa da su, suna aikin tsintar tunatur ne a gonakansu, lokacin da 'yan bindigar suka farma musu, suna harbin kan mai uwa da wabi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China