Moussa Faki Mahamat, ya bayyana haka ne yayin rufe taron kungiyar da ya gudana daga ranar 17 zuwa 18 ga wata, a hedkwatar kungiyar dake Addis Ababa na Habasha .
Ya kara da cewa, harkokin duniya na sauyawa, don haka ya kamata a samar da matsaya guda ta nahiyar tare da yin magana da murya guda.
Ya kuma bayyana cewa tabarbarewar alakar kasa da kasa da ke zama abun damuwa a duniya, ya haifar da bukatar samar da matsaya guda ta nahiyar.
A cewarsa, yayin da sauye- sauyen al'amuran duniya a yanzu ke tasiri kan nahiyar, bukatar tabbatar da 'yancin kan kungiyar AU da ma nahiyar baki baya, abu ne mai muhimmanci.
Har ila yau, Faki Mahamat, ya bayyana yayin taron majalisar zartarwar kungiyar na 20 da aka yi ranar Larabar da ta gabata cewa, sauyen sauyen da ake fuskanta na nuni da bukatar karfafa kungiyar. (Fa'iza Mustapha)