Babbar jami'ar sashen kula da tattalin arzikin karkara da harkokin gona ta hukumar AU Leah Wanambwa, ta shaidawa taron MDD kan kyautata rayuwar halittu cewa, dabarar za ta taimakawa kasashen daidaita kokarinsu na kare hallitun daji a Afrika.
A cewarta, sabuwar dabarar za ta rage yawan amfani da su da kuma cinikinsu ta haramtacciyar hanya, wadanda ke haifar da raguwar adadin nau'ikan halittun daji irinsu giwaye da rhinos.
Ta ce an samar da dabarar ne biyo bayan amincewa da wata manufa kan halittun daji da shugabannin nahiyar suka yi a shekarar 2015, ta na mai cewa a farkon bana kuma, shugabannin gwamnatoci da kasashe mambobin AU, suka amince da dabara da ke da nufin inganata kokarin magance amfani da halittun dajin ta hanyar da ba ta dace ba.
Taron MDD kan kyautata rayuwar halittu na bana, wanda ke gudana daga ranar 13 zuwa 29 ga watan nan a birnin Sharm El-Sheikh na Masar, mai taken 'kokarin kyautata rayuwar halittu domin mutane da duniya', ya samu halartar kimanin kasashe 196. (Fa'iza Mustapha)