Wata sanarwa da ministan lafiyar ya fitar ta nuna cewa, hana amfani da wannan sinadari a daukacin fadin kasar ya taimaka, wajen dakile matsalar shaye shaye tsakanin al'ummar kasar, tare da baiwa masu shaye shayen damar farfadowa, da kyautata rayuwar su.
Sinadarin "codeine" dai dangi ne na sinadaran "morphine" da "hydrocodone" wadanda ake amfani da su wajen kashe zafin ciwo, da maganin tari.
An haramta amfani da sinadarin ne a Najeriya, tun daga ranar 1 ga watan Mayun bana, sakamakon yadda ake yawaita amfani da shi wajen maye.
Masana a fannin lafiya sun yi ta kiraye kiraye, game da hana amfani da wannan sinadari, duba da yadda mutane da dama suka raja'a wajen amfani da shi a matsayin sinadarin sa maye maimakon magani. (Saminu)