Cikin taron da aka yi a wannan rana, bangarorin biyu sun cimma ra'ayi daya a kan cewar, za a karfafa musayar al'adu a tsakanin Sin da Indiya wadda za ta tallafawa kasashen biyu a kokarinsu na neman raya kansu. Ya kamata kasashen Sin da Indiya su kara musayar dake tsakaninsu bisa tsarin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, kasashen BRICS, hadin gwiwar kasashen gabashin Asiya da kuma dandalin tattaunawar kasashe masu dogon tarihi da dai sauransu, ta yadda za a ba da gudummawa wajen inganta zaman lafiya da ci gaba na shiyyar da suke ciki, har ma na kasashen duniya baki daya. (Maryam)