in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta soki matakin Indiya na gina hanyoyi a kusa da kan iyakar da aka shata
2017-08-24 20:18:59 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta shaidawa taron manema labarai a yau Alhamis a nan birnin Beijing cewa, matakin kasar Indiya na gina hanyoyi a kusa da kan iyakar da aka shata ya ci karo da abin da Indiyan ke fada da abin da take aikatawa a zahiri.

Madan Hua ta bayyana hakan ne yayin da take karin haske game da shirin kasar Indiya na ginawa sojojinta hanyoyin mota a kusa da yankin yammacin da aka shata.

A cewar jaridar Hindustan Times, ma'aikatar harkokin cikin gidan Indiya ta bayar da aikin gina hanya daga wurin wanka na Marsimik La to mai nisan kilomita 20 daga arewa maso yammacin tafkin Pangong kwanaki kadan bayan da sojojin sassan biyu suka fara aikin fasa duwatsu a tafkin Pangong dake Ladakhs,

Madan Hua ta ce, wadannan rahotanni tamkar zubar kimar Indiya ne, kuma hakan ya nuna cewa, Indiyan tana kwan gaba kwan baya sannan tana saba kalamanta wajen warware takaddama kan iyakar da ta kunno kai tsakanin Sin da Indiya.

Ta ce, matakin Indiya na ginawa sojoji kayayyakin more rayuwa a kusa da yankin yammaci da aka shata, ba zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a sashen yammaci na kan iyakar ba, kana ba zai taimaka wajen rage zaman tankiya tsakanin sassan biyu ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China