in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin kiyaye adalci kan lamarin shiga yankin kasar Sin da sojojin Indiya suka yi
2017-08-02 17:05:57 cri

A yau ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wata takarda mai lakabin "yadda sojojin kasar tsaron kan iyaka na kasar Indiya suka ketare zangon Sikkim dake kan iyakar dake tsakaninta da kasar Sin suka shiga cikin yankin kasar Sin da kuma matsayin kasar Sin dangane da lamarin", inda ta kara yi wa kasashen duniya bayani kan gaskiyar lamarin, tare da bayyana matsayinta daga dukkan fannoni.

Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, kasar Sin ta dauki wannan mataki ne domin kare yankunanta, kiyaye muhimman dokokin kasa da kasa da raya hulda a tsakanin kasashen duniya, da kiyaye adalci. Kasar Sin ta yi imani da cewa, babu wanda bai san gaskiyar lamarin ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China