Kasashen Sin da Indiya za su iya tuntubar juna ta hanyar diplomasiyya ko a'a? Ko za su ci gaba da warware batun ta hanyar diplomasiyya ko a'a? Game da batun, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Litinin a nan Beijing cewa, kasar Sin ta sake bukatar Indiya da ta janye sojojinta daga yankin kasar Sin a matsayin sharadi na farko, kana tushen da kasashen 2 za su tuntubi juna da yin tattaunawa a tsakaninsu. Kasar Sin na fatan Indiya za ta dauki hakikanin matakan da suka dace don warware wannan batu cikin ruwan sanyi. (Tasallah Yuan)