in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole ne Indiya ta dauki alhakin shigar sojojinta kasar Sin
2017-08-03 20:57:04 cri

Yau Alhamis ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya amsa tambayoyin manema labaru dagane da lamarin shigar sojojin kasar Indiya yankin kasar Sin.

Geng Shuang ya ce, ya zuwa yammacin ranar 2 ga wata, jami'an Indiya 48 da wata babbar mota sun kutsa yankin kasar Sin ba bisa ka'ida ba. Ban da haka kuma, tarin sojojin Indiya sun yi cincirido a bangaren Indiya dake bakin iyakar kasar da Sin.

Ya ce sojojin Indiya da dama sun ketare bakin iyakar kasa su, inda suke ci gaba da taruwa a bangaren kasar Sin, wanda hakan ke nuna Indiya ta keta ikon mallakar yankin kasar ta Sin, tare da saba wa kundin tsarin MDD, da dukkanin dokoki. Kuma wajibi ne kasar ta dauki alhakin wannan laifi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China